China: Kamfanin Apple ya Goge Manhajar Al-Ƙur’ani Daga App Store
Kamfanin Apple ya goge manhajar Al-Ƙur’ani mai tsarki ta Quran Majeed daga shagon manhajojinsa na App Store a China bayan gwamnatin ƙasar ta nemi ya yi hakan.
Ana ci gaba da samun manhajar Quran Majeed a sauran sassan duniya a shagon na App Store, wadda aka yi tsokaci a kanta sau kusan 150,000. Miliyoyin Musulmai ne ke amfani da manhajar.
BBC ta fahimci cewa an goge manhajar ce saboda tana ɗauke da wasu litattafan addini da ba a amince da su ba a China.
Sai dai gwamnatin China ba ta amsa buƙatar da BBC ta aike mata ba don mayar da martani.
Quran Majeed manhaja ce mai ɗauke da abubuwan Musulunci da suka haɗa da lokutan sallah da sautin karatun Ƙur’ani na malamai daban-daban da wasu litattafai da ke koyar da addinin.
Kamfanin PDMS da ya ƙirƙiri manhajar ya ce: “A cewar Apple, an goge manhajarmu Quran Majeed daga kasuwar China saboda tana ɗauke da wasu abubuwa da gwamnatin China ba ta kammala duba su ba.”