Gombe ta Cire Kakakin Majalisar Dokokin Jahar
Bayan kasa da shekara daya kan kujerar, an tunbuke kakakin majalisa.
Wanda aka cire kafin ya hau ne ya jagoranci cire Kakaki.
Ba tare da bata lokaci ba aka nada sabon Kakaki.wanda zai jagoranci majalisar.
Mambobi sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Gombe, Abubakar Ibrahim Kurba, tare da shugaban masu rinjaye a majalisar, Samuel Markus Markwina.
Tsohon mataimakin kakakin, Shuaibu Adamu, wanda aka tsige shekarar nan ne ya gabatar da bukatar tsige Kakakin.
Shuaibu Adamu ya karanto takardar tsige Kakakin bayan mambobi 16 cikin 24 sun rattafa hannu.
Read Also:
An alanta Abubakar Muhammad Luggerewo, mai wakiltar mazabar Akko ta tsakiya, matsayin sabon Kakakin Majalisar, yayinda aka sanar da Yarima Gaule mai wakiltar Kaltungo ta gabas matsayin sabon shugaban masu rinjaye.
Jawabi ga manema labarai, bulaliyar majalisa, Musa Buba ya yi bayanin cewa an tsige Abubakar Kurba ne saboda yana sabawa dokokin majalisar.
“Tsohon Kakakinmu ya kasance mai karya dokokin majalisa, saboda haka aka yanke shawaran tsigeshi kawai,” Musa Buba yace.
Daily Sun ta tattaro cewa gabanin tsige kakakin, an yi rikici yayinda aka tura yan baranda hana wasu mambobi shiga majalisar.
Da kyar suka samu suka shiga kuma suka tsigeshi.