Sheikh Kabiru Gombe ya Yafewa Muaz Magaji Kan Kalaman da ya yi a Shafinsa na Facebook
Bayan bada hakuri a Facebook, Muaz Magaji yayi takakkiya zuwa wajen Kabiru Gombe.
Malamin yace ya yafe masa kuma yayi kira ga jama’a su yafe masa.
Malam Gombe yace yanzu sun kulla zumunci da dan sarauniya.
Abuja – Sakataren Janar na Jama’atu Izalatul Bid’a wa iqamatus-Sunnah, Malam Kabiru Haruna Gombe, ya bayyana cewa ya yafewa Muaz Magaji, tsohon kwamishanan ayyukan Kano.
Malam Gombe ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook da yammacin Asabar, 11 ga Satumba, bayan karban bakuncin Muaz Magaji.
Magaji yayi tattaki har zuwa gidan Malamin kuma ya gana da shi don bashi hakuri ido da ido.
Kabiru Gombe yace:
Read Also:
“A yammacin asabar dinnan tsohon kwamishinan ayyuka na jahar Kano, Honourable Muazu Magaji ya ziyarce mu a gida domin bada hakuri tare da janye kalamansa da yayi a shafinsa na Facebook. Ya kuma yi sa’a ya same mu da shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau.
Munyi hakuri, mun yafe masa, kuma mun kulla zumunci. Allah ya kiyaye gaba.
Ina kira ga sauran ‘yan uwa abokan gwagwarmaya da kuma ku yafe masa, domin Allah yana son masu yafiya.”
Ya yi barazanar shigar da shi kotu
Zaku tuna cewa babban Malamin yayi barazanar shigar da tsohon kwamishanan Ganduje, Muazu Magaji kotu.
Kabiru Gombe ya yi watsi da maganar da Muazu Magaji ya daura a shafinsa na Facebook cewa ya nadi waya tsakanin Kabiru Gombe da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress APC.
A cewarsa, shi Malamin addini ne kuma bashi da alaka da wata jam’iyya a Najeriya kuma shi ba dan siyasa bane.
Muaz Magaji ya nemi gafara
Tsohon kwamishanan ayyukan Kano, Muaz Magaji wanda akafi sani da Win-Win Dan Sarauniya, ya nemi gafarar Malam a sakon da ya daura shafinsa na Facebook.
Ya ce ba shi ya kirkiri labarin ba, a wata jarida ya gani.