Gomes ya yi Watsi da Tayin West Ham , Arsenal na Son Kean
Dan wasan tsakiya na Lille da Ingila Angel Gomes, mai shekara 24, ya yi watsi da tayin da West Ham ta yi masa, duk da cewa kungiyar ta yi masa tayin kwantaragin biyansa fam dubu 100,000 a kowane mako idan kwantaraginsa ya zo karshe a wannan bazara . (Guardian), external
Arsenal na zawarcin na sha’awar sayan dan wasa mai kai hari na Florentina da Italiya , Moise Kean mai shekara 25 wanda a baya bai yi nasara ba a Everton (Tuttomercatoweb – in Italian, external)
Manchester United ta saka ‘yanwasa masu kai hari biyu na Bundesliga watau dan wasan RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21, da dan wasan Eintracht Frankfurt da Faransa Hugo Ekitike, mai shekara 22 a cikin jerin sunnayen ‘yan wasan da za su nema a bazara. (Sky Sports, external)
Haka kuma Man Utd na son dan wasa tsakiya na RB Leipzig da Netherlands, Xavi Simons, mai shekara 21, wanda a baya ta so ta dauko kafin ya koma Jamus da taka leda a watan Janairu . (Sky Sports, external)
Real Betis za su gana da Manchester United domin tattauna makomar dan wasan gefe na kasar Brazil Antony, mai shekara 25, wanda ya nuna kwazo sosai a lokacin da aka bada shi aro ga La Liga. (ABC – in Spanish, external)
Read Also:
Liverpool ta kara kaimi a zawarcin da ta ke yi wa dan wasan baya na Bournemouth da Hungary Milos Kerkez, mai shekara 21, wadanda suka bayana a matsayin wanda zai maye gurbin Andy Robertson na tsawon lokaci. (i, externalpaper)
Bournemouth za ta bukaci dan wasan baya na kungiyar Club Brugge da Belgium Maxim de Cuyper, mai shekara 24, idan suna son su maye gurbin Kerkez. (Football Insider, external)
Atletico Madrid ta ce dan wasan gaba na Argentina Julian Alvarez, mai shekara 25, ba dan wasan da za ta sayar bane duk da cewa cewa Liverpool tana sha’awarsa. (Mirror, external)
Dan wasan gefe na Chelsea da Ingila England Noni Madueke, mai shekara 23, zai je AC Milan a matsayin aro a wannan bazara. (Fichajes, external)
Wataila Chelsea ta sayar da ‘yan wasa 11 a wannan bazara ciki harda dan wasa gaba, Raheem Sterling, mai shekara 30, da dan wasa mai tsaron baya Ben Chilwell mai shekara 28 domin samun kudin daukar sabon dan wasa mai kai hari . (Mail+ – subscription required, external)
Barcelona na son ta sake dauko dan wasan gaba na Argentina da Inter Miami Lionel Messi, mai shekara 37. (TNT Sports, external)
Dan wasan baya na Real Madrid dan kasar Sfaniya Raul Asencio, mai shekara 22, na shirin Sanya hannu kan sabon kwantiragi na dogon lokaci da kungiyar ta Sfaniya. (Fabrizio Romano, external)