Yakubu Gowon ya Karyata Maganar da Aka Fada Akansa

Gowon ya mayar da martani ga dan majalisar dokokin Birtaniya wanda ya zarge shi da sace rabin kudin CBN a 1975.

Tsohon shugaban kasar a mulkin soja ya karyata zargin, inda ya bayyana shi a matsayin “shirme” kuma ba gaskiya ba .

Tom Tugendhat, ya yi zargin ne a lokacin da takwarorinsa ke muhawara kan wata kara game da zanga-zangar #EndSARS.

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya yi martani a kan zargin cewa ya sace rabin kudin babban bankin kasar a lokacin ya yi balaguro zuwa birnin Landan bayan an yi masa juyin mulki a watan Yulin 1975.

Tom Tugendhat, wani dan majalisar Birtaniya, yayi zargin a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, lokacin muhawara a kan wata kara da ke kira ga hukunta jami’an gwamnatin Najeriya da ake zargi da hannu wajen cin zarafin yan EndSARS.

Gowon, a martaninsa, ya bayyana zargin dan majalisar a matsayin “shirme”. Kamar yadda sashin BBC ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasar ya ce ya bauta wa Najeriya bisa gaskiya da tsoron Allah, inda yace ayyukan da ya yi ba boyayyu ba ne don haka kowa yana iya zuwa ya gan su.

Ya kara da cewa shi bai san wanda ya dauki nauyin dan majalisar domin yin irin wannan zargi a kansa ba.

Gowon ya kara da cewa shi ba zai kara cewa komai kan lamarin ba domin wadanda suka san shi sosai sun fahimci cewa zargin ba gaskiya bane.

Gowon ya shugabanci Najeriya daga 1966 zuwa 1975. An yi masa juyin mulki a yayinda ya je Kampala, kasar Uganda halartan wani taro na kungiyar hadin kan Afrika.

Daga can ne kuma ya tafi Ingila, inda ya zama dalibi a Jami’ar Warwick University.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here