Janar Gowon ya Magantu Kan Jita Jitar Mutuwarsa

 

Janar Yakubu Gowon, tsohon shugaban kasa na mulkin soja a Najeriya ya yi magana kan rahotannin cewa ya riga mu gidan gaskiya.

Tsohon shugaban na Najeriya ta bakin hadiminsa a bangaren watsa labarai ya ce lafiyarsa kalau kuma yana nan da ransa kana ba gaggawa barin duniya ya ke yi ba.

Gowon ya mulki Najeriya ne daga watan Agusta na shekarar 1966 zuwa 29 ga Yulin shekarar 1975 kuma a zamaninsa kasar ta tsinduma yakin basasa da masu neman kafa Biyafara.

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya karyata rahoton cewa ya mutu kamar yadda wasu kafafen watsa labarai suka wallafa.

A cikin wani sako da NTA ta fitar a kafar X, hadimin tsohon shugaban mulkin sojan ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya ce lafiyarsa kalau kuma yana nan da ransa, ya kara da cewa ba gaggawar mutuwa ya ke ba.

Ga sakon a kasa:

Ya ce:

“Ina nan har yanzu kuma lafiya ta kalau. Ba gaggawa na ke ba”

Gowon shine shugaban mulkin soja na uku a Najeriya bayan kasar ta samu yancin kai a shekarar 1960.

A lokacin mulkinsa ne kasar ta tsinduma cikin yakin basasa, wacce aka shafe watanni 30 ana tafkawa.

Tsohon shugaban na mulkin soja wanda ya jagoranci kasar tsakanin 1 ga watan Agustan 1966 zuwa 29 ga Yulin, 1975, yana cikin wadanda suka kafa kwamitin zaman lafiya ta kasa a 2005.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com