Gwamnatin Najeriya Ba Ta Goyon Bayan Soke NYSC – Ministan Matasa.

 

Gwamnatin Najeriya ta jaddada rashin goyon bayanta game da shirin rushe yiwa ƙasa hidima na National Youth Service Corp (NYSC) biyo bayan yunƙurin da ‘yan Majalisar Dattawan ƙasar ke yi na soke shi.

Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare, ya ce NYSC na “ɗaya daga cikin hanyoyin ci gaban ƙasa”.

“Ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ci gaba da aiwatar da shirin yana nan daram,” a cewarsa cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sai dai ya ce suna kan duba hanyoyin da za a kawo gyara don shirin ya dace da abin da ake da shi a ƙasa.

Bisa dokar ƙasa a Najeriya, duk ɗalibin da ya kammala karatu matakin digiri ko babbar difiloma zai je aikin hidimar ƙasa na NYSC matuƙar bai wuce shekara 30 ba.

BBC Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here