Ba’a Gudanar da Zaɓen Fitar da ɗan Takara ba a Jahar Anambra – Ministan ƙwadugo

Danbarwa ta ɓarke a jam’iyyar APC reshen jahar Anambra biyo bayan bayyana wanda ya lashe zaɓen fitar da ɗan takara.

Ministan ƙwadugo, Chris Ngige, yace kwata-kwata ba’a gudanar da wani zaɓe ba a jahar, ya kuma bada shawarar 29 ga watan Yuni.

Kakakin APC reshen jahar, Okelo Madukaife, ya nesanta jam’iyyarsa da sakamakon da ake yaɗawa

Rikici ya ɓarke a jam’iyyar APC biyo bayan bayyana, Sanata Andy Uba, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamnan Anambra dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba, kamar yadda punch ta ruwaito.

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani kuma gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, shine ya bayyana sakamakom zaɓen a Otal ɗin Tulip, Awka da safiyar Lahadi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamna Abiodun yace Uba shine ya lashe zaɓen fidda gwani da ƙuri’u 230,201 yayin da ya lallasa na kusa da shi, Johnbosco Onunkwo, wanda ya samu ƙuri’u 28,746.

Ngige yace Ba’a gudanar da zaɓen fidda ɗan takara ba Ministan ƙwadugo da samar da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa sam ba’a gudanar da zaɓen fitar da ɗan takara ba.

Ministan ya baiwa jam’iyyar APC shawarar ta shirya zaɓen fitar da ɗan takara a ranar 29 ga watan Yuni.

Hakazalika, 11 daga cikin mutum 14 dake neman jam’iyyar APC ta tsayar da su takara sun bayyana cewa ba’a gudanar da zaɓen ba.
APC a Anambra ta yi watsi da sakamakon zaɓen da ake yaɗawa

A wani jawabi da kakakin jam’iyyar APC reshen jahar Anambra, Okelo Madukaife, ya fitar, ya nesanta jam’iyyarsu da rahoton zaɓen da ake yaɗawa.

Yace:

“An jawo hankalin mu kan wani rahoto dake yawo a kafafen watsa labarai ba tare da sanya hannun kowa ba, kuma ana danganta shi da sakamakom zaɓen fidda ɗan takara na jam’iyyar APC a Anambra.”

“Sakamakon ba shi da alaƙa da zaɓen fidda ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan Anambra, wanda kwata-kwata ba’a gudanar da shi ba.”

“Muna jiran kwamitin riƙo na APC ta ƙasa ya saka ranar zaɓen cikin jadawalin da hukumar zaɓe ta fitar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here