Ana Gudanar da Zanga-Zanga Cikin Lumana a Legas

 

Tituna sun zama kufai yayin da bankuna da shaguna suka kasance a rufe a fadin jihar Legas daidai lokacin da yan Najeriya suka fara zanga-zangar adawa da matsin rayuwa.

Masu zanga-zangar na ihun “a kawo karshen gwamnati mara nagarta” inda wasu ke rike da alluna yayin da suka hallara a Ikeja.

Tuna tattaki zuwa dandelion Freedom Park, data data caking wuraren da koto ta amince a yi zanga-zangar.

Akwai kuma tawagar jami’an tsaro da aka girke a gaba da bayan daruruwan masu zanga-zangar domin hana afkuwar rikici.

Sai dai masu zanga-zangar sun bayyana cewa suna yin ta ne a lumana don kawo karshen matsin rayuwa da neman a dawo da tallafin mai da inganta tsaro da sauran garambawul da dama da suke neman gwamnati ta yi.

Akwai raisin tabbas game da zanga-zangar, abin da watakila ya shafi fitowar wasu zuwa wuraren zanga-zangar saboda gudun abin da ka je ya zo.

Masu zanga-zangar dai sun tsara yin ta tsawon kwana 10 har asian biya masu bukatunsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here