An Tarwatsa Masu Zanga-Zanga a Kano

 

Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin Najeriya, dubban matasa a jihar Kano sai kara fitowa suke daga unguwanni suna taruwa a kan titin gidan gwamnati.

Wakilin BBC a Kano ya ruwaito cewa matasan rike da alluna suna ta furta kalmomin “Ba ma yi” inda ya ce wasu matasan na komawa gida suna sake shiri.

A cewarsa, ana fargabar an harbi mutum uku cikin masu zanga-zangar.

Jami’an tsaro kuma a wasu wuraren sun zama yan kallo sannan sun janye motocin su ƙanana.

Jami’an tsaro sun yi amfani da barkono mai sa hawaye a ƙoƙarin tarwatsa masu zanga-zanga waɗanda ke tattaki zuwa a kusa da fadar sarkin Kano da ke unguwar Nassarawa.

Tun da safe ne masu zanga-zangar nuna fushi kan matsin rayuwa suka fito a birnin, inda suka fara daga Gidan Murtala, suka ce za su yi tattaki zuwa gidan gwamnati.

Da farko zanga-zangar ta fara cikin lumana, sai dai daga baya abubuwa sun fara rincaɓewa a lokacin da jami’an tsaro suka yi yunƙurin tarwatsa masu zanga-zangar wadanda suka dumfari gidan gwamnati.

Bayanai na cewa jami’an tsaro sun yi harbi da bindiga a kan masu zanga-zangar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here