Yadda Shugaban Makaranta ya Gudu da kuɗin WAEC ɗin ɗalibai a Jahar Edo

 

Wani bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda aka shanya wasu ɗalibai yayin da suka zo zana jarabawar WAEC.

Makasudin haka shi ne shugaban makaranta ya tattara kuɗin rijistar WAEC daga hannun ɗalibai kuma aka neme shi aka rasa.

Bidiyon ya yi bayanin cewa lamarin ya faru ne a jihar Edo kuma fusatattun ɗaliban sun rage fushinsu a kan Tagunan harabar makaranta.

Edo – Wani shugaban makaranta wanda har yanzun ba’a gano bayanansa ba ya tattara kuɗin jarabawar fita daga Sakandire WAEC daga bisani aka neme shi aka rasa a jihar Edo.

A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta wanda Legit.ng Hausa ta gani, shugaban makarantar bai yi wa ɗaliban da suka bashi kuɗi rijista ba, ya shnya su a ranar farko ta fara jarabawa.

A cikin Bidiyon an ga ɗaliban da ke ajin ƙarshe a babbar Sakandire wato SS 3, waɗan da ya dace ace suna cikin aji suna jarabawa, sun fusata suna aika-aika a harabar makarantar.

Rahotanni sun bayyana cewa mamallakin makarantar ya sa ta a kasuwa ƙamar yadda mutane suka ga an kafa allon sanarwa a babbar kofar shiga harabar wurin.

An hangi ɗaliban suna jifan ginin makarantar da abubuwa daban-daban, suna farfasa tagogi kuma suna karya kayayyakin makaranta.

Mutane sun yi martani a Istagram

@naomikamara92 ya ce:

“Abun ba dadi amma ya ba ni dariya sosai, ba na mamakin duk abin da mutanen mu na Benin suka yi ba domin za su iya mafi haka.”

@Hypegad ya ce:

“Ƙannen mu sun rasa goben su dai a nan wurin, wannan abun tsoro ne.”

@ngfabs ya ce:

“Shin wannan wasa ne? Wane kalan wasa ne wannan?”

@oluwa_soji7 ya ce:

“Ba abun kunyar da bazaka gani ba a kasar nan ta mu Najeriya duk ƙanƙantar shi.”

@chigozie_ehim1 ya yi martani da cewa:

“Kamata ya yi a kama shi cikin gaggawa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here