An Gurfanar da Diezani Alison-Madueke a Gaban Kotu Kan Cin Hanci
‘Yan sandan Burtaniya sun gurfanar da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan cin hanci.
‘Yan sandan sun bayyana haka a ranar Talata 22 ga watan Agusta yayin da su ke zarginta da karbar na goro.
Madueke ta kasance tsohuwar shugabar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC) a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Read Also:
Landan – Wani sabon rahoto ya tabbatar da cewa ‘yan sanda a Burtaniya sun gurfanar da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan cin hanci.
Wannan na zuwa ne bayan yin bincike da Hukumar Laifuka ta Kasa (NCA) ta yi kamar yadda Reuters ta tattaro.
NCA ta ce Diezani ta karbi cin hanci a lokacin da ta ke rike da mukamin ministar man fetur don karbar kwantiragi na miliyoyin Daloli, Legit.ng ta tattaro.
Ana zargin ta samu kusan Yuro dubu 100 da wasu motoci da kuma jiragen hawa don shakatawa da iyalanta da kuma amfani da wasu kadarori na birnin Landan.