An Gurfanar da Malamin Jami’ar Jahar Kwara a Gaban Kotu Bisa Zargin sa da Yunkurin Yin Lalata da Dalibarsa
Pelumi Adewole, malamin jami’ar jahar Kwara, ya gurfana gaban wata kotun majistare da ke zama a Ilori bisa zargin sa da yunkurin yin lalata da dalibarsa.
Ofishin leken asirin jahar na zargin sa da laifuka ciki har da yunkurin lalata da magudin jarabawa bayan ya ce zai fadar da dalibarsa.
matukar taki amincewa da bukatar sa An rawaito yadda lamarin ya auku a watan Satumban 2021, wanda laifin na sa ya yi daidai da yanki na 397 da 95 dokar Panel Code a kan magudin jaraba na gwamnatin tarayya.
Kwara – Pelumi Adewole, malami a jami’ar jahar Kwara ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke zama a Ilorin, jahar Kwara bisa zargin sa da yunkurin kwanciya da wata dalibarsa.
Ofishin leken asirin jahar ya gabatar da Adewole gaban kotu bisa ruwayar The Cable akan yunkurin cutar da dalibarsa da magudin jarrabawa tare da sauran laifuka yayin da ya yi ikirarin fadar da dalibar matukar ta bijire wa bukatarsa.
Read Also:
Lamarin ya auku ne a watan Satumban 2021, wanda ya ci karo da sashi na 397 da 95 na Panel Code Law da sashi na 3(320) na magudin jarabawa Act Cap. E15 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 2004 wanda dokar ta tanadi hukunci.
An umarci dalibar da ta yi aiki da ‘yan sandan jahar don samar da hujjoji gamsassu. Kungiyar lauyoyi mata ta tarayya reshen jahar Kwara ta bayyana cewa:
“Malamin ya bukaci dalibar ta bayyana a dakin sa da misalin karfe 8:30 na dare a layin Taoheed, yankin Basin da ke Ilorin, inda ya ba ta tambayoyin jarabawar KWASU da amsoshin su don ta rubuta jarrabawar bisa sharadin za ta bari ya yi lalata da ita har sai asuba ta yi.
“Daga nan jami’an ofishin leken asirin jahar su ka kama wanda ake zargin bayan sun boye a wurin.”
Lauyan masu karar ya bukaci kotu ta hana belin wanda ake zargin
Bayan Adewole ya ki amsa laifukan da ake zargin sa, Mai gabatar da kara, Nasir Yusuf ya kula da yadda yunkurin lalata da dalibai ya yi yawa a jami’o’in kasar nan.
Bayan nan, Yusuf ya bukaci kotu ta rike malamin sakamakon munin laifin nasa.
Lauyan Adewole, A.J. Opalekunde ya bukaci kotu ta bayar da belin sa sakamakon yadda ba a kama shi dumu-dumu da laifin ba.
Alkalin kotun, Ibrahim Mohammed ya bukaci N200,000 a matsayin belin wanda ake karar sannan ya gabatar da tsayayye.
Daga nan ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Disamban 2021 don ci gaba da sauraro.