‘Yan Sanda Sun Gurfanar da Matashi ɗan Shekara 25 Bisa Zargin sa da Kashe Mahaifiyarsa a Jahar Oyo
Rundunar yan sanda reshen jahar Oyo, ta gurfanar da wani matashi ɗan shekara 25, Solomon, bisa zargin kashe mahaifiyarsa.
Rahoton yan sanda ya nuna cewa wanda ake zargin ya tura mahaifiyar tasa ne cikin rijiya saboda tace masa babu abinci a gida.
Jami’an yan sanda sun samu nasarar kama wanda ake zargin ne bayan samun rahoto daga yan uwansa.
Oyo – Rundunar yan sanda reshen jahar Oyo, ta gurfanar da wani matashi ɗan kimanin shekar 25 a duniya, Solomon Ochadi, a gaban kotun majistire dake zamanta a Ibadan, bisa zarginsa da hallaka mahaifiyarsa, Elizabeth Ochadi.
Punch ta rahoto cewa rundunar yan sandan ta gurafanar da manomin matashin ne kan zargi ɗaya tal, na kisan kai.
Karamin sufetan yan sanda, mai gabatar da ƙara, Opeyemi Olagunju, ya faɗa wa kotun cewa wanda ake zargin ya ingiza mahaifiyar tasa ne cikin rijiya.
Read Also:
Yace hakan ya yi sanadiyyar mutuwar matar yar kimanin shekara 50, wacce take uwa a gare shi, a cikin rijiya.
Meyasa ya tura mahaifiyarsa cikin rijiya?
Da yake labartawa kotu yadda lamarin ya faru, mai gabatar da ƙara na rundunar yan sanda yace wanda ake zargin ya nemi abincinsa daga mahaifiyar tasa bayan ya dawo daga gona.
Yace:
“Matar ta shaida masa cewa babu abinci a gidan. Ba zato sai ya ingizata cikin rijiya saboda fushi da amsar da ta ba shi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.”
Bayan kasheta, su waye suka tona asirinsa?
Olagunju, ya cigaba da shaidawa kotu cewa bayan ya kashe ta, Solomon ya nemi wuri a bayan gidansu ya yi wa gawarta ƙabari.
Kannen matashin, da suka ganewa idonsu abinda ya faru, sune suka sanar da yan sanda, kuma aka cafke wanda ake zargin, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Wane mataki kotu ta ɗauka?
Majistire Olaide Hamzat, yace kotu ba ta da hurumin yanke hukunci kai tsaye, domin akwai bukatar a gudanar da bincike.
Bisa haka ne ya bada umarnin a kai fayil da kuma shaidu zuwa hukumar zartar da hukunci domin shawarwari kuma ya ɗage zaman zuwa 23 ga watan Nuwamba.