An Gurfanar da Mutane 47 a Amurka Kan Zargin Almundahanar $250m na Tallafin Corona

 

Masu shigar da ƙara a Amurka sun gurfanar da mutum 47 kan rawar da ake zargin sun taka wurin almundahanar dala miliyan 250 da aka ware domin ciyar da yara abinci a lokacin Corona.

Daraktan hukumar FBI Christopher Wray ya bayyana wannan lamari da ya faru a Minnesota a matsayin almundahana mafi girma kan kayayyakin corona.

Waɗanda ake zargin an bayyana cewa sun karɓi kuɗi daga gwamnati na abincin da ba su bayar ba ga yaran da babu su.

Ana zargin wata ƙungiya mai zaman kanta ce ta shirya almundahanar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here