Ebonyi: Gwamna ya Fatattaki Hadimansa na Musamman a Kan Tsaro
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya kori hadimansa na musamman da ke fannin tsaro.
Read Also:
Ya hada da wasu manyan jami’ansa uku sakamakon kone ofisoshin ‘yan sanda da aka yi . Gwamnan ya ce ya yi hakan ne saboda rashin kwarewarsu a fannin tsaron da ya saka su Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori hadimansa na musamman da ke bashi shawara a kan tsaro da wasu jami’ai uku a kan kone ofisoshin ‘yan sanda da wasu kadarorin gwamnati a jihar. A wata takardar da ta fito daga sakataren gwamnatin, Kenneth Ugbala, a ranar Lahadi, ya ce mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai, Nchekwube Aniakor da wasu shugabanni uku, ya sallamesu. Shugabannin da aka sallama sun hada da Amos Ogbonnaya, Jerry Okorie Ude da Martha Nwankwo.
A wuraren ne ‘yan daba suka kai wa ofisoshin ‘yan sanda hari a Abakaliki, babban birnin jihar a ranar Laraba. Bata-garin sun tarwatsa wasu kayayyakin gwamnati ballantana na kan tituna a sassa daban-daban na jihar. Ugbala ya ce gwamnan a kokarinsa na ganin tsaro ya tabbatar a jihar ne ya kori hadimansa, Premium times ta wallafa.