APC: Gwamnan Rivers Yayi Martani Kan Takarar Goodluck Jonathan a 2023
Gwamnan jahar Rivers, Nyesome Wike ba zai goyi bayan Goodluck Jonathan ba idan ya yi takarar shugaban kasa a APC.
Wike ya ce duk da cewa dukkansu mutanen kudu ne, ba zai taba iya juyawa jam’iyyarsa ta PDP baya ba domin kabilanci.
Wike ya kuma soki Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, saboda kiransa ma’aikacinsa inda ya ce ta dalilinsa ne Amaechi ya zama gwamna.
Gwamnan Rivers, Nyesome Wike ya ce ba zai mara wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan baya ba ko da ya samu tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023, rahoton The Nation.
Read Also:
A hirar da ya yi da BBC Pidgin a karshen mako a Port Harcourt, gwamnan ya kuma ce Allah ya yi amfani da shi wurin nada Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, zama gwamnan Rivers.
Wike ya ce ko shi Jonathan ya ce cewa shi (Wike) zan juya masa baya idan ya shiga APC ya kuma samu tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2023.
Ya ce: “Ni dan PDP ne, Idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu tikitin takarar shugabancin kasa a jam’iyya ta, zan mara masa baya.
Amma idan ya samu tikitin a APC, ba zan goyi bayansa ba domin ba zan ci amanar jam’iyya ta ba.
“Ya san cewa ba zan mara masa baya ba a APC duk da cewa daga Kudu ya fito. Bana irin wannan siyasar. Jam’iyya muke magana ba kabilanci ba.”
Wike ya kuma soki Amaechi saboda kiransa ma’aikacinsa inda ya ce Ministan Sufurin ya zama gwamnan jahar Rivers ne saboda Allah ya yi amfani da shi (Wike) a matsayin sanadi ba.