Gwamnan Jahar Abia ya yi Martani Kan Barin Jam’iyyar PDP
Gwamna Okozie Ikpeazu ya magantu a kan rade-radin cewa yana shirin sauya sheka.
Ikpeazu ya ce sam bai ga dalilin da zai sa ya bar PDP zuwa wata jam’iyya ba.
Ya kuma jadadda cewa sune da karfi a jihar Abia.
Gwamnan jihar Abia, Okozie Ikpeazu ya bayyana cewa ba zai sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).
Da yake watsi da rade-radin sauya shekar, ya ce batun bai da tushe saboda PDP ce jam’iyya mafi rinjaye a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.
Read Also:
Da yake magana a Umuahia, babbar birnin jihar, Ikpeazu ya ce bai ga dalilin da zai sa ya bar PDP zuwa wata jam’iyya ba.
Ya ce: “Ban ga dalilin da zai sa na bar PDP zuwa wata jam’iyyar siyasa ba. Yadda ake murza kambun siyasa a kowani jiha ya banbanta da juna.
“A nan Abia, mutanen sun gamsu da PDP kuma ina ganin takarar Ndi Abia zai cimma nasara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.”
Ikpeazu ya kara da cewa: “Babu wanda ya iya gamsar dani cewa akwai wata jam’iyya a nan Abia da ta fi PDP. Ni babban dan PDP ne kuma jigo a jam’iyyar.
“Bugu da kari, ni ne mataimakin Shugaban kungiyar gwamnonin PDP. Na gwammaci na zama kwandastan mota da na zama direban motar da bata tafiya.”