Daga Dukkan Alamu Wani Gwamnan Arewa Zai Canza Jam’iyya

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya taya Dave Umahi na jihar Ebonyi murnar ficewa daga jam’iyyar PDP.

Matawalle ya bayyana cewa akwai wasu matsaloli a jam’iyyar ta PDP wadda sune sukayi sanadin Umahi ya fice daga jam’iyyar.

Matawalle ya ce bai ga laifin Umahi ba don idan ba a maraba da mutum a wuri ba zai iya cigaba da zama ba.

Gwamnan Zamfarar ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnonin kudu maso kudu suka shiga kafafen watsa labarai suna yada karya kan gwal din Zamfara.

Gwamman Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yabawa takwararsa na Jihar Ebonyi, David Umahi da ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC.

Mista Matawalle ya alakanta ficewar Mista Umahi daga PDP ta “rashin jituwa tsakanin mambobin jamiyyar ta Peoples Democratic Party”.

Gwamnan Zamfaran, wanda dan jam’iyyar PDP ne ya yi wannan jawabin ne ta bakin mai magana da yawunsa, Zailani Bappa a ranar Juma’a kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mista Matwalle ya ce ya gwammace ya jinjinawa Mista Umahi “kan babban matakin da ya dauka a maimakon sukarsa domin mutum na iya zama ne a gidan da ake maraba da shi.”

“Idan wannan rashin jituwar ya cigaba da wanzuwa ba a magance shi ba, jam’iyyar mu ce za ta cigaba da fuskantar matsala a yayin da muke tunkarar zaben 2023,”a cewar Gwamna Matawalle.

“Ina fuskantar kallubalai a baya-bayan nan daga wasu takwarorina na PDP kuma hakan na daure min kai.

Misali, gwamnonin PDP na Kudu maso Kudu sun shiga kafafen watsa labarai suna ruruta wutar batun gwal din Zamfara bisa rashin fahimta da karerayi,” inji Gwamna Matawalle.

“Abin mamaki, gwamnatin tarayya ta APC ce ta fito ta bayyana gaskitar lamarin kan hakkar gwal din ta kare ni a kan batun.

A matsayinsu na ‘yan uwana na PDP, ina tsammanin zasu tuntube ni don jin ta baki na kafin su fara yada maganganu marasa dadi a kafafen watsa labarai,” in ji shi.

Gwamna Matawalle ya yabawa gwamnatin tarayyar Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari bisa goyon bayansa wurin tsara bangaren tattalin arzikin jiharsa don kare amfani da ma’adinan wurin janyo fitintinu a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here