Gwamnan Bauchi ya Musanta Zance Barin Shi Jam’iyyar PDP
Gwamna Bala Mohammad na Jihar Bauchi ya musanta raɗe raɗin cewa zai fice daga jam’iyyar PDP.
Gwamnan ya bayyana cewa duk wani batu dangane da canjin sheka ko zaɓen 2023 abu ne da zai kawo tsaiko wajen cika alkawarin da ya dauka lokacin yaƙin neman zabe.
Ya shawarci jama’a suyi watsi da rahoton tare da jaddada aniyarsa na inganta rayuwar al’ummar Bauchi ba tare da nuna bambanci.
ba Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam’iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam’iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A wata sanarwa ranar Juma’a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam’iyya mai mulki.
Read Also:
“Muna so mu sanar cewa wannan labarin karya ne da aka kirkira saboda wata bukata ta kashin kai, don jawo hankali masu bibiyar labaran siyasa wanda ficewar gwamnan Ebonyi ya sake ta’azzara labarin siyasar ƙasar,” a cewar Gidado.
Ya ƙara da cewa, “muna su mu sanar da cewa mai girma Gwamna Sanata Bala Mohammad bai taɓa kokonton barin PDP zuwa APC ba.
“Sai dai, yanzu yana tsaka da cika alkawuran da ya ɗauka lokacin yakin neman zaɓe, wanda akan haka al’ummar Bauchi suka goya masa baya ya kifar da gwamnati mai ci.”
Don haka, Gwamna Bala Mohammed yana ɗaukar magana akan canja jam’iyya da zance akan 2023 a matsayin abin da zai ɗauke masa hankali,” kamar yadda Gidado ya bayyana.
Saboda haka, gwamnan yana shawartar masoyansa sa, ƴan jam’iyyar PDP da al’ummar Bauchi da suyi watsi da rahoton.
Ya kuma jaddada aniyarsa na inganta rayuwar al’umma mazauna Bauchi ba tare da nuna bambanci ba.