Yadda Gwamnan Jahar Benue Yayi Gudun Ceton Ransa a Gurin ‘Yan Bindiga

 

Gwamnan Benuwai ya tabbatar da cewa ‘Yan bindiga sun kai masa hari a cikin jeji.

Hadimin Samuel Ortom ya ce ba kirkirar labarin kanzon-kurege gwamnan ya yi ba.

Terver Akase ya ce Gwamnan ya yi gudun kilomita ne saboda ya bar motarsa a nesa Gwamnatin jahar Benueta bayyana cewa za ta bada hadin-kai domin jami’an tsaro su binciko wadanda su ka nemi su hallaka gwamna Samuel Ortom.

Gwamnatin Benue ta kuma yi karin-haske, ta ce ba a sama kurum aka kirkiro labarin harin da aka kai wa Mai girma Samuel Ortom a ranar Asabar ba.

The Nation ta rahoto babban sakataren yada labaran gwamnan, Terver Akase, ya na bayanin ainihin abin da ya faru da gwamnan a makon da ya wuce.

Hadimin ya ce: “Gwamna bai gana da masu bincike ba tukuna. Mu na sa ran zuwansu. Gwamna ya nuna shirinsa na hadu wa da su, za mu ba su goyon-baya.”

“Gwamna Ortom ba kirkiro labarin nan ya yi ba. Shakka babu, an kai masa hari. Jami’an tsaro sun tabbatar an nemi a hallaka gwamnan.” Inji Terver Akase.

A cewar Terver Akase, babu abin da zai sa gwamnan ya nemi suna ta hanyar kirkiro labarin kashe shi. “Eh, ya yi gudun sama da kilomita daya zuwa inda aka ajiye motocinsa. Inda gonarsa ta ke kusa da yankin kogin Benue ne, ba za a iya shiga da mota ba.”
“Saboda haka dole aka je da kafa, a hanyar dawowansu ne aka yi masu sameme.

Jami’an tsaron da ke tare da shi sun yi kokari, su ka kare harin da aka kawo.”

“Kwarai, bajintar jami’an tsaron da ke tare da shi ne ya ceci shi a ranar. Mu na gode wa Allah.”

Akaase ya ce ‘yan bindigan ba su ci karfin jami’an tsaronsa ba.

Akaase ya fito ya yi bayanin ne bayan wasu sun fara karyata rahotonnin, su na cewa ba zai yiwu ace gwamna ya sharara tsawon kilomita guda ya na gudu ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here