Gwamnan Benue ya Mika Bukatarsa Gurin Gwamnatin Tarayya
Gwamnan jihar Benue ya mika babbar bukata gaban shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamna Ortoma ya bukaci shugaban kasa kada ya cire takunkumin hana shigo da shinkafa daga waje.
Ortom ya lissafa abubuwan da aka ribatu da su sakamakon sanya takunkumin tsawon shekara daya da yan watanni.
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari kada ya saurari maganan mutane na cire takunkumin hana shigo da shinkafar gwamnati daga kasashen waje.
Read Also:
The Punch ta ruwaito cewa gwamna Ortom ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ranar Litinin, 30 ga Nuwamba.
Ya yabawa shugaba Buhari kan dokar yayinda ya ambaci muhimman riba biyu da aka ci tun lokacin da aka hana shigo da shinkafa.
A cewar gwamna Ortom, hana shigo da shinkafa ya harzuka manoman shinkafan gida da kuma noma gaba daya a jihar.
Ya ce wannan ne abu guda babba da gwamnatin Buhari tayi.
Gwamnan ya bayyana cewa duk da cewa za’a fuskanci matsaloli da wahala na dan lokaci, manoma na samun kudi sosai yanzu fiye yadda suke samu a baya.
Wani dalilin da gwamnan ya ambata shine samarwa matasa aikin yi. Ya ce matasa da dama sun koma noma kuma hakan ya taimaka.
Ortom ya ce idan aka cigaba a haka, jihar Benue za ta rika samawa kasar gaba daya abinci.