Gwamnan Jahar Borno ya Mika Gwamnatin jahar Na Tsawon Kwanaki 21 ga Mataimakinsa
Gwamnan jahar Borno Farfesa Babagana Zulum ya mika gwamnatin jahar ga mataimakinsa Usman Kadafur.
Zulum ya mika gwamnatin na tsawon kwana 21 ga Kadafur ne domin ya samu daman zuwa hutu.
Gwamna Zulum ya umurci dukkan ma’aikatan gwamnati da hukumomi a jahar su bada cikaken hadin kai bisa mika mulkin.
Majalisar dokokin jahar Borno ta amince mataimakin gwamnan jahar Umar Usman Kadafur ya yi aiki a matsayin gwamna na rikon kwarya daga ranar 29 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Mayun 2021.
Read Also:
Hakan na zuwa ne sakamakon hutu na kwanaki 21 da Gwamna Babagana Zulum zai tafi kamar yadda gwamnatin jahar ta sanar a shafinta na Twitter.
Kakakin majalisar dokokin jahar Borno, Abdulkarin Lawan ne ya sanar da amincewar majalisar a wasika mai dauke da kwanan wata na 26 ga watan Afrilu.
Zulum ya rubutu wasikar neman samun amincewar majalisar ne a ranar 23 ga watan Afrilun 2021 domin ya samu ya tafi hutun kwanaki 21.
Sashi na 190 (1) na kudin tsarin mulki ya bukaci gwamnan ya nemi izinin majalisar dokokin domin nada mataimakin gwamna ya yi aiki a matsayin gwamna na rikon kwarya domin ya samu ikon gudanar da mulki a jahar ba tare da ya tuntubi gwamna ba.
“Gwamnan ya umurci dukkan ma’aikatan gwamnati da hukumomi su bada cikaken hadin kai bisa mika mulkin da ya yi ga mataimakinsa,” a cewar kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau.