An Kuma: Gwamnan Ebonyi Ka Kori Wasu Jami’ansa

Gwamna Umahi na jihar Ebonyi ya fatattaki wasu jami’ai 2 masu kula da kananan hukumoni a kan rashin goyon bayansa.

Sun ki sanya hannu a wata takarda wacce ya nemi duk wani mabiyinsa ya saka hannu a kai don barranta daga Anyim.

Wadanda ya kora sun ce ba za su mara masa baya su ci zarafin Anyim ba, wanda kowa ya san babban mutum ne Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya fatattaki wasu jami’an kula da kananun hukumomi 2.

Dama ya fara fatattakar ma’aikata tun bayan ya canja sheka.

Ya kori Okorie Daniel na Ivo DC da Fabian Ivoke na Echiele DC, saboda kin amincewa da wata takarda da suke tunanin za ta bata sunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim.

Anyim abokin tafiyar Umahi ne, kafin ya koma jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP, a ranar 20 ga watan Nuwamba, Premium times ta wallafa.

Manyan mutanen Ivo sun taru a Abakaliki ranar Laraba don su mara wa gwamnan baya akan canja shekar da yayi.

Tsofaffin ‘yan majalisar tarayya da na jiha, da kuma wadanda har yanzu suke kan mulki, da sauran manyan mutane sun samu damar halartar taron.

Manyan mutanen Ivo sun taru a Abakaliki ranar Laraba don su mara wa gwamnan baya akan canja shekar da yayi.

Tsofaffin ‘yan majalisar tarayya da na jiha, da kuma wadanda har yanzu suke kan mulki, da sauran manyan mutane sun samu damar halartar taron.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here