Aikin Hajji: Gwamnan Jahar Kano ya Bawa Maniyyatan Jaharsa Shawara
Gwamnan jahar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kirayi maniyyatan hajjin bana da su zama jakadun ƙasar nan nagari a lokacin gudanar da aikin.
Gwamnan ya yi wannna kira ne a ya yin da yake jawabi a wajen buɗe taron bita da ƙara wa juna sani da aka shiryawa mahajjatan bana, 2020/2021.
A cewarsa, yana fatan mahajjatan Kano su zama masu kyawawan ɗabi’u a ya yin gudanar da aikin su.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano ya yi kira ga mahajjatan bana na jahar Kano da su zama wakilan ƙasar nan nagari, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a ya yin jawabinsa a wajen buɗe taron ƙarawa juna sani da aka shirya ma mahajjatan bana a jahar, 2020/2021.
Read Also:
Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jahar, Alhaji Usman Alhaji, ya wakilta yace an shirya taron ne saboda a haskaka ma mahajjata da ilimantar dasu akan yadda ake aikin hajji a addinance.
Ya kuma ƙara da cewa muna fatan maniyyatan mu zasu yi abun da zai haskaka kasar mu a lokacin da suke a ƙasa mai tsarki.
“Muna fatan maniyyata aikin hajjin bana zasu zama masu kyawawan ɗabi’u a lokacin gudanar da aikin su.” inji shi.
A ɓangarensa, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero, ya bayyana cewa: “Ko kaɗan bamu ji daɗin rashin samun damar yin aikin hajji ba a shekarar 2020 saboda ɓullar annobar COVID19.”
Daga ƙarshe, sakataren hukumar kula da jin daɗin alhazai na jahar Kano, Alhaji Muhammed Dambatta, ya yabawa gwamnatin jahar bisa goyon bayan da take bawa hukumar sa.