Gwamnan Jahar Kogi ya Nada Mai Aikin Share-Share a Matsayin Babban Mai Taimaka Masa Kan Tsafta

 

Gwamna Bello na jahar Kogi ya nada Peter Aliyu, mai aikin share-share, a matsayin babban mai taimaka masa kan tsafta.

A cewar SSG na jahar, an nada Aliyu ne saboda kwazo da jajircewarsa.

Har zuwa lokacin da aka nada shi, Aliyu ya kasance mai shara a karkashin shirin tsafta na Geemoney a jahar Kogi.

Daga aikin share-share a karkashin shirin hadin gwiwa na gwamnatin jahar Kogi, Geemoney Cleaning Scheme, Peter Aliyu ya daukaka ya zama Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Yahaya Bello kan Tsafta.

An sanar da nadin Aliyu ne a wata sanarwa da Sakatariyar Gwamnatin Jahar (SSG), Dakta Folashade Arike Ayoade, ta sa wa hannu, aka kuma aika wa Legit.ng a ranar Asabar, 8 ga Mayu.

An sanar da nadin Aliyu wanda ke da matsalar magana a majalisar zartarwar jahar tare da sauran sabbin wadanda gwamnatin ta bai mukamai a cikin gwamnatin jahar.

Me yasa aka nada Aliyu Da yake bayyana dalilin nadin na Aliyu, SSG din ya ce Gwamna Bello ya gamsu da yadda matashin ya kasance mai kwazo, himma da jajircewa bayan lura da shi na wani lokaci.

Sakatariyar ta lura cewa halayen da Gwamna Bello ya lura su sun kuma sa Aliyu yana burge mutane da yawa wadanda suka yaba da nadin nasa.

Dokta Ayoade ta kara da cewa Gwamna Bello bai dauki nakasar Aliyu na rashin iya magana, “a matsayin cikas gareshi ba illa ya dauki hakan a matsayin wata hanya ta shigar da shi da kuma tabbatar wa duniya cewa gaskiya ne batun cewa a nakasa ma akwai iyawa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here