Gwamnan Jahar Nasarawa ya Fadi Dalilin Zuwansa Amurka
Gwamnan Jahar Nasarawa Injiniya Abdullahi Abdullahi ya bayyana cewa ziyarar sa Amurka bata da alaka da duba lafiya..
Ya shaida cewa ya dauki hutun karshen shekara kamar yadda ya saba kuma ya tafi hutawa tare da iyalan sa a Houston da ke Texas.
Ya kuma kara da cewa yayi amfani da damar wajen yin gwajin lafiya kamar yadda ya saba tun kafin zaman sa gwamna amma lafiyar ƙalau.
Gwamnan Jahar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya karyata jita jitar da ke cewa ya tafi Amurka ne don duba lafiyarsa, ya kuma bayyana cewa yaje Amurka don ziyartar yayan sa yayin da ya ke hutun karshen shekara.
Read Also:
Gwamnan ya yi ikirarin ne lokacin da ya bayyana a hirar gidan talabijin na Channels, kamar yadda kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Sule, wanda ake ganin ya wofantar da asibitocin jihar don tafiya duba lafiya zuwa Amurka, ya bayyana cewa yana daukar hutun shekara a watan Disamba kuma yayi amfani da wannan damar don ziyartar iyalan sa a Houston, Texas.
Gwamnan ya kara da cewa yayin da ya ke hutu a Amurka, inda ya dauki tsawon lokaci, ya yi amfani da damar don duba lafiyarsa.
“Ziyara ta nan bata da alaka da lafiya. Nazo ne hutun karshen shekara. Kamar yadda na saba, ana duba lafiyata tun lokacin ina babban daraktan kamfanonin Dangote.
“Ba abin da ke damuna, lafiya ta ƙalau. Na kammala gwajin lafiya kamar yadda na saba, hakori, ido da komai kuma komai lafiya ƙalau,” ya yi karin bayani.