Dalilan da Yasa Wani Gwamnan PDP Zai Koma APC
Dave Umahi, gwamnan Jihar Ebonyi ya shaidawa shugabannin jam’iyyar PDP cewa zai fice daga jam’iyyar.
Jam’iyyar APC mai mulki itace inda yake shirin komawa saboda yana ganin cewa zasu bawa dan yankinsa ta kudu takara a 2023.
Amma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa a jam’iyyar ta PDP matukar zasu bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya gaya wa shugabancin jam’iyyar PDP a Abuja ranar Talata cewa zai bar jam’iyyar.
Ya ce zai koma jam’iyya mai mulki ta APC yana mai ikirarin cewa APCn zata bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara a zaben 2023.
Umahi ya kuma bayyana cewa ya riga ya yanke shawara kuma bazai chanja ba.
Shugabannin da suka jagoranci taron sune, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus wanda shi ya jagoranci taron sun yi kokarin gamsar da gwamnan kada ya bar jam’iyyar amma a banza.
Read Also:
Baya ga Secondus, wanda suka halarci taron a gidan gwamnan Ebonyi da ke Abuja, akwai mataimakin Sakataren PDP Agbo Emmanuel, Sakataren tsare tsare Austin Akobundu, da sauran Shugabannin jam’iyya.
Gwamnan yaji dadin yadda ya karbi bakoncin shugabannin PDP amma hakan bai sa ya fasa ya janye kudirinsa ba.
Shugabannin sun gaya masa babu bukatar ya bar jam’iyyar don komawa APC.
Wata majiya ta ce, gwamnan bai gamsu ba, yana ikirarin APC din tana shirin bawa dan yankin sa takarar shugabancin kasa.
Yayi alkawarin zama a PDP matukar zasu bawa dan yankin sa takara.
Daya daga cikin majiyar ta ce, “ina ji ya riga ya gama zartar da hukunci.
Mun fada masa babu bukatar ya bar jam’iyyar da ta kai shi matakin mataimakin gwamna, shugaban jam’iyya a jaha, gwamna har sau biyu, amma duk da haka yaki yarda.
“Yana so ne dole sai mun damka kujerar takarar shugabancin kasa ga yankin sa.
Baza mu iya haka ba.
Ba haka ake tafiyar da jam’iyya ba.
Ya ce mana zai bar jam’iyya.
Wannan ne abun da muka samu daga gareshi.
“Da aka tuntube shi, Secondus ya tabbatar da cewa shugabannin jam’iyya sun gana da Umahi.
Sai dai, bai bayyana komai dangane da taron ba, yana ikirarin taron anyi ne akan abin da ya shafi kasa.