Gwamnan Jahar Rivers ya Bawa Iyanlan Jami’an ‘Yan Sanda 11 da ‘Yan Bindiga Suka Kashe Kyautar N20m
Gwamnan jahar Rivers, Nyesom Wike, ya bada gudummuwar miliyan 20 ga kowane ɗaya daga cikin iyalan jami’an yan sanda 11.
Gwamnan yace babu wani kuɗi da zai iya maye gurbin ran ɗan adam .
Kwamishinan yan Sandan jahar, Friday Eboka, ya yabawa gwamnan bisa wannan kulawa.
Gwamna Nyesom Wike na jahar Rivers, ya bada kyautar 20 miliyan ga kowane ɗaya daga cikin iyalan jami’an yan sanda 11 da aka kashe a hare-haren da yan bindiga suka kai musu a faɗin jahar.
Gwamnan, wanda ya sanar da haka yayin da yakai ziyarar ta’aziyya ga kwamishinan yan sandan jahar, Friday Eboka, a hedkwatar hukumar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Read Also:
Lokacin da yake jawabi ga jami’an yan sandan a Patakwal, gwamna Wike yace ya kawo musu ziyara ne domin ya jajanta musu bisa rashin wasu daga cikin abokan aikinsu, waɗanda suka rasa rayuwansu a ƙoƙarin kare jahar.
Gwamnan ya ƙara da cewa duk da babu wasu kuɗi da zasu yi dai-dai da ran mutum, amma tallafin gwamnatin jahar zai tabbatarwa iyalan mamatan cewa yan uwansu basu mutu hakanan ba.
Yace: “A makwanni biyu zuwa uku da suka gabata, mun rasa jami’an yan sanda 11, wannan lokaci ne mai muni a wajen mu.”
“Waɗanda ke wannan ɗanyen aikin sun mayar da matan jami’an zawarawa, yayin da suka maida yayan su marayu, ba tare da wani dalili ba.”
A nasa ɓangaren, kwamishinan yan sandan jahar, amadadin muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alkali Baba, ya yabawa gwamnan bisa nuna kulawarsa ga iyalan jami’an da suka rasu.