Gwamnatin Tarayya ta Dakatar da Biyan Albashin Ma’aikata 3,000
Gwamnatin Najeriya ta ce ta gano ma’aikata 1,500 da suka gabatar da takardun shaidar ɗaukar aiki na boge ga kwamatin da ta kafa na tantance ma’aikata.
Shugabar Ma’aikatan Gwmanatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, ita ce ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta shirya a Abuja ranar Talata.
Read Also:
Ta ce gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan albashin ma’aikata 3,000 da suka gaza bayyana a gaban kwamatin don tantancewa.
An ƙaddamar da shirin ne don bankaɗowa da kuma korar ma’aikatan da suka shiga aikin ba ta hanyar doka ba, a cewarta.
“Wani lokaci a watan Maris na 2021, wannan ofis ɗin ya faɗa wa ICPC cewa akwai wasiƙun ɗaukar aiki masu yawa da ke zagaye a ma’aikatu,” in ji ta kamar yadda Channels TV ta ruwaito ta tana faɗa.
“A lokacin, mun gano cewa a ma’aikata ɗaya kacal, akwai masu ɗauke da wasiƙun boge 1,000, kuma tuni aka saka su cikin masu karɓar albashi.”