Gwamnatin Najeriya za ta Daukaka ƙara Kan Nnamdi Kanu
Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba hukuncin da kotu ta yanke na yin watsi da ƙarar da gwamnati ta shigar kan shugaban kungiyar IPOB, mai rajin ƴantar da yankin Biafra.
Kotu a ranar Alhamis ne ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da ake yi wa Mr Kanu, inda ta bayar da hujjar cewa yadda aka dawo da shi Najeriya ya saɓa wa doka.
Sai dai a sanarwar da ofishin ministan shari’a na ƙasar ya fitar ta ce kotun ta yi watsi ne da ƙarar kawai, amma ba ta wanke shi daga laifukan da ake tuhumarsa ba.
Read Also:
Hakan na nufin cewar da yiwuwar ba za a saki Nnamdi Kanu nan take ba, sai dai lauyoyinsa na iƙirarin cewar wajibi ne gwamnati ta saki Kanu kasancewar kotu ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi masa kafin ta ɗauki duk wani mataki na gaba.
A ranar 29 ga watan Yuni na shekarar 2021 ne gwamnatin Najeriya ta dawo da Nnamdi Kanu Najeriya ta gurfanar da shi a gaban kotu, inda bayanai ke cewa an kama shi ne a ƙasar Kenya.
Sannan hukumar tsaron ciki ta DSS ta samu izinin ci gaba da tsare shi a hannunta.
Nnamdi Kanu dai shi ne jagorar ƙungiyar ƴanta yankin Biafra, wadda gwamnatin Najeriya ta haramta.