Cutar Lassa: Gwamnatin Tarayya Na Cikin Fargaba

Gwamnatin tarayya ta shiga cikin matsananciyar fargaba sakamakon cutar Lassa da ta kunno kai a wasu jahohin Najeriya.

Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya tabbatar da yadda cutar ta fara barna musamman a ‘yan makonnin nan har ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

A jihar Delta, an samu masu cutar guda 23, wasu 17 kuma sun rasa rayukansu, yayin da mutane 51 suka mutu a jihar Enugu sakamakon zazzabin cutar Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta a kan yadda masu zazzabin cutar Lassa a wasu jihohin Najeriya suka yawaita.

Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya bayyana yadda hankalinsa ya tashi, a Abuja lokacin taron PTF a kan cutar da kuma COVID-19.

A cewarsa, an samu sababbin masu zazzabin Lassa a wasu jahohi, musamman a lokacin ranin nan, Vanguard ta wallafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here