Ina da Yakinin Cewa Gwamnati Mai ci za ta yi Nasara a Kokarinta na Tsaron Kasa – Garba Shehu
Fadar shugaban kasa ta yi martani kan matsalolin tsaro a Najeriya.
Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana abunda Buhari ke yi don magance matsalolin tsaro.
Shehu yana da yakinin cewa gwamnati mai ci za ta yi nasara a kokarinta na tsaron kasar.
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke fuskantar kalubale wajen kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
Read Also:
Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya ce matsalolin tsaro a kasar na rikedewa, saboda haka yake kara tabarbarewa.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Shehu ya bayyana hakan ne a yayinda ya bayyana a shirin Television Continental (TVC) a ranar Lahadi, 10 ga watan Janairu.
Sai dai ya ba yan Najeriya tabbacin cewa shugaban kasar na aiki tukuru don tsare kasar.
Ya ce:
“Kasar nan na fama da matsalolin rashin tsaro a koda yaushe. Babu kasar da bata fama da laifuka. Matsalolin na rikidewa… amma duk ana iya bakin kokari a yanzu.”
Shehu ya ce Buhari ya jajirce don magance Boko Haram, fashi da makami da sace-sacen mutane a 2021.