ENDSARS: Gwamnati ta Lissafa Muhimman Wuraren da Mabarnata Suka Lalata

Har yanzu ana cigaba da samun sabbin rahotannin tafka ta’annati da mabarnata ke yi a sassan Nigeria.

Mabarnata na cigaba da kai farmaki wurare daban-daban mallakar gwamnati da daidaikun mutane – Gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa muhimman wurare 22 mabarnata suka lalata a ‘yan kwanakin baya bayan nan Gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa muhimman wurare 22 mabarnata suka lalata a ta’adin da batagari ke cigaba da yi a sassan Nigeria

Batagarin matasa sun fake da zanga-zangar ENDSARS wajen fara balle wuraren ajiya mallakar gwamnati da daidaikun mutane da kuma shiga gidajen manyan ‘yan siyasa tare da yin awon gaba da duk kayayyakin da ke ciki. Ana zargi cewa wasu batagarin matasa sun kwace iko da zanga-zangar ENDSARS domin tafka barna da sauran miyagun laifuka.

Mabarnatan matasa sun tafka barna a mafi yawan manyan shagunan ajiye kayan abinci mallakar gwamnati da daidaikun jama’a da ke sassa daban-daban na Najeriya. Matasan da ke tafka wannan barna suna kwashe dukkan kayayyakin da suka samu a irin wadannan manyan shaguna. A yayin da matasan ke ikirarin cewa suna kwashe kayan abincin da gwamnati ta bayar da sunan tallafin korona, rahotanni sun wallafa yadda mabarnatan ke kwasar duk abinda hannunsu ya taba, koda ba mai amfani garesu ba.

A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar Filato ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa wurare 22 mabarnta suka lalata ta hanyar konawa ko kuma ragargazasu. Gwamnan jihar Filato tare da mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun ziyarci ginin ‘JIB Complex’, gidan tsohon shugaban majalisa, Yakubu Dogara, da kuma ofishin hukumar gyara hanyoyi ta jihar Filato da mabarnata suka lalata.

Macham Machut, kakakin gwamna Lalong ya ce; “mambobin majalisar wakilai tare da gwamna Lalong sun ziyarci wuraren da mabarnata suka lalata a Jos da Bukuru a ‘yan kwanakin baya bayan nan. Ba mu ji dadin abinda ya faru ba”. Ya ce rikicin ya mayar da jihar Filato baya tare da dora mata nauyin gyara wuraren da mabarnata suka lalata a jihar.

A cewar Mista Machut, gwamna Lalon ya bukaci jama’a suke kare gine-ginen gwamnati da ke makwabataka da su, ya ce yin hakan zai karawa gwamnati karfin guiwa wajen cigaba da shimfida aiyukan raya kasa.

A cewar Mista Machut, gwamna Lalon ya bukaci jama’a suke kare gine-ginen gwamnati da ke makwabataka da su, ya ce yin hakan zai karawa gwamnati karfin guiwa wajen cigaba da shimfida aiyukan raya kasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here