Legas: An Kashe Wasu  ‘Yan Sanda  Tare da Raunata Wasu  Yayin Zanga-Zangar Endsars 

 

   Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce an kashe jami’anta shida tare da raunata 38 sakamakon barkewar rikici a zanga-zangar nuna adawa da cin zalin ‘yan sanda a jihar Legas.

   Kwamishinan rundunar a jihar Legas Hakeem Odumosu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

  Ya ce jami’an da aka kashe sun hadar da Yard Edward da Olayinka Erinfolami, da Adegbenro Aderibigbe da Abejide Abiodun da wasu karin mutum biyu.

   An samu mummunan tashin hankali a jihar ta Legas, bayan da bata gari suka mamaye jihar suna kone-kone da lalata gine-ginen gwamnati, lamarin da ya janyo kafa dokar hana fita ta tsawon kwanaki

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here