Gwamnatin Tarayya ta Raba wa ‘Yanƙwadago da ɗalibai Motoci 64 Masu Amfani da Gas

 

Gwamnatin Najeriya ta miƙa wa ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da ku ma ta ɗalibai NANS motocin bas masu amfani da iskar gas 64 a jiya Lahadi.

An gudanar da bikin miƙa motocin ne a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja a matsayin wani ɓangare na bikin cika shekara 64 da samun ‘yancin kai.

Da yake magana yayin bikin, Ministan Kuɗi Wale Edun ya ce wannan ɗaya ne daga cikin yunƙurin gwamnatin na sauƙaƙa farashin zirga-zirga wanda ya hauhawa tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.

“Babban abin da muka saka a gaba shi ne zirga-zirgar jama’a,” in ji ministan.

Ya ƙara da cewa hikimar ba da motocin a jajiberin bikin ‘yancin kai ita ce saka ɗambar fito da su da yawa, yana mai cewa sun tsara raba sama da 500 da kuma masu amfani da lantarki 100.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here