Gwamnatin Tarayya ta Sanar da Siyar da Iskar Gas Kan N250 ko Wace Lita

 

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sanar da siyar da iskar gas a kan Naira 250 ko wace lita.

Gwamnatin Tarayya ta bukaci mutane su mayar da ababan hawansu zuwa masu amfani da iskar gas.

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke siyan litar man fetur daga Naira 580 har zuwa Naira 640 a fadin kasar.

FCT, Abuja – Shugba Bola Tinubu ya sanar da siyar da iskar gas a kan Naira 250 a kan ko wace lita daya.

Hadimin shugaban, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce sun shirya kawo sauki a kasar.

Meye Tinubu ya ce kan amfanin Gas?

Iskar gas din ita za ta maye gurbin bakin mai da kuma man fetur da mutane ke amfani da su a harkokinsu na yau da kullum, Legit.ng ta tattaro.

Ngelale ya ce Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da cewa an yi amfani da iskar gas din a madadin man fetur don samun sauki ga al’umma.

Ya kara da cewa tsarin wanda shugaban ma’aikata, Femi Gbajabiamila ke jagoranta zai samar da motoci dubu 11,500 masu amfani da iskar gas don kawo sauki a sufuri.

Wane tsari Tinubu ke yi kan Iskar gas?

Ya ce:

“Wannan tsari ya na da matukar muhimmanci ga Tinubu saboda rage amfani da fetur kuma ‘yan Najeriya na shan wahala kan hauhawan farashin kayayyaki.

“Shi ne dalilin da yasa Tinubu ya kawo wannan tsari don rage wahalhalu a bangaren sufuri ga ‘yan Najeriya.”

Ya ce gwamnati za ta yi kokarin inganta tsarin samar da shi don karya farashin litar man fetur.

Ya kara da cewa:

“A nan tsammanin ku biya Naira 250 a ko wace lita na iskar gas, hakan zai karya farashin mai da ake siya a kan Naira 620 ko wace lita daya.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com