Hukumar Tace Finafinan Jihar Kano ta Kulle Sutudiyon Mawaƙi Idris Danzaki

 

Sutudiyon mawaƙi Idris Danzaki ya sha garƙama a hannun jami’an hukumar tace finafinai da ɗab’i ta jihar Kano.

Hukumar ta garƙame sutudiyon mawaƙin na siyasa ne bayan ya yi biris ya ƙi amsa gayyatar da ta yi masa.

Mawaƙin ya bayyana cewa bai san laifin da hukumar take zarginsa da aikatawa ba, duk da wasu rahotanni na cewa ya ɗan taɓa Kwankwaso ne a waƙarsa.

Jihar Kano – Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta jihar Kano ta garƙame sutudiyon mawaƙin siyasar nan, Idris Danzaki, tare da yin awon gaba da kayan da yake gudanar da aikinsa.

Hukumar ita ce ta tabbatar da hakan ta hannun jami’in hulɗa da jama’anta, Abdullahi Lawan Sulaiman, inda ya ce an kulle sutudiyon mawaƙin ne bayan ya yi kunnen uwar shegu da gayyatar da ta yi masa, cewar rahoton Aminiya.

Ya bayyana cewa hukumar ta buƙaci mawaƙin ya bayyana a ofishinta tun ranar Asabar, amma sai ya yi biris ya ƙi amsar gayyatar da ta yi masa.

Abdullahi ya bayyana cewa bayan hukumar ta kira mawaƙin ya bayyana a gabanta, sai ya turo lauyansa ya bincika masa cewa ko da gaske ne hukumar tana nemansa.

Hakan ya sanya shugaban hukumar Abba El-Mustapha ya buƙaci a ƙara gayyatar mawaƙin, amma duk da haka bai amsa wannan gayyatar ba.

Abdullahi Lawan ya kara da cewa hakan ya sa hukumar ta sanya aka kulle sutudiyon tare da kwashe kayayyakin aikinsa.

Danzaki ya yi martani

A yayin da jaridar ta tuntubi mawaƙin ya tabbatar da cewa hukumar ta gayyace shi, amma bai amsa gayyatar ba, ya dai tura lauyansa domin ya wakilce shi.

Ya bayyana cewa bayan ya tura lauyan nasa kawai sai aka kira shi a waya ake gaya masa cewa hukumar ta kulle sutudiyonsa tare da kwashe wasu daga cikin kayan aikinsa.

Danzaki ya yi iƙirarin cewa hukumar ba ta gaya masa ainihin laifin da take zargin ya aikata ba.

Duk da har yanzu hukumar ba ta bayyana dalilin gayyatar mawakin ba, wasu rahotanni sun nuna cewa hukumar na zarginsa ne da yin kalamai munana akan madugun ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Mawaƙin dai ya yi kalaman ne a cikin wata waƙa da ya fitar a kwanakin baya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com