Gwamnatin Zamfara ta yi Afuwa ga Fursunoni 31

 

Jihar Zamfara – Gwamnatin jihar Zamfara ta yi afuwa ga wasu fursunoni da ke gidan gyaran hali na Gusau.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa dole a saka ido ga kurkuku musamman yadda ake kara kama yan bindiga a jihar.

Mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal, Sulaiman Bala Idris ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.

Gwamnan Zamfara ya yi afuwa ga fursunoni

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi afuwa ga fursunoni 31 da ake kulle da su a gidan gyaran hali na Gusau.

Mai girma Dauda Lawal ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi damar yin afuwa ga fursunoni.

Dalilin sake fursunoni a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa a yanzu haka ana kama yan bindiga da dama a jihar kuma ana kai su kurkuku.

Saboda haka ya ce dole a rika daukar matakin rage cunkoso kuma hakan ne ya saka shi yin afuwa ga fursunonin su 31.

Gwamna ya yi kyauta ga fursunoni

Biyo bayan sakin fursunonin, gwamna Dauda Lawal ya ba kowane ɗaya daga cikinsu kyautar kuɗi N50,000.

Gwamnan ya ce kudin zai taimaka musu wajen rage raɗaɗi idan suka koma cikin al’umma da zama.

Shugaban gidan yarin Gusau, Dr Umar Galadima ya yabawa gwamna Dauda Lawal bisa kokarin da ya yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here