Gwamnatin Jahar Borno Zata Gina Jami’a Mai Zaman Kanta a Jahar

Gwamna Zulum na Jihar Borno ya aza harsashin gina jami’ar Al-Ansar, jami’a mai zaman kanta a jahar Borno ranar Litinin.

Gwamnan ya kuma ce a shirye gwamnatin sa take ta tallafawa duk wani mai son taimakawa bangaren ilimi a jahar.

Dr Muhammad Kyari Dikwa shi ne shugaban gidauniyar Al-Ansar kuma wanda ya samar da jami’ar, ya yabawa gwamnatin Zulum bisa tallafawa bangaren ilimi.

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Litinin ya aza harsashin gina jami’ar Al-Ansar, jami’a ta farko mai zaman kanta a jahar.

Zulum wanda gwamnatin sa ta bada fili mai girman hekta 100 ga gidauniyar Al-Ansar don gina jami’ar, ya kuma umarci da a gina titi mai nisan kilo mita 2.3 da kuma bohol a jawabin da ya gabatar wajen taron.

Zulum ya kuma umarci ma’aikatar ilimi mai zurfi da su bibiyi wanda ya samar da jami’ar don ganin yadda gwamnati zata iya ci gaba da tallafawa aikin.

Gwamnan wanda ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tallafawa ilimi a jihar, yayi alkawarin tallafawa duk wani mai yunkurin samar da ingantaccen ilimi a Borno.

“A shirye muke mu tallafawa duk wani mutum ko kungiya da ke son hada hannu da gwamnatin mu wajen samar da ingantaccen ilimi a kowane mataki,” a cewar Zulum.

A nasa jawabin, wanda ya samar da jami’ar kuma shugaban gidauniyar Al-Ansar, Dr Muhammad Kyari Dikwa, ya bayyana cewa za a fara jami’ar da bangarori biyu.

Dr Dikwa ya yabawa gwamnatin Zulum bisa yadda take tallafawa bangaren ilimi tare da tabbatar da cewa zasu taimaka wajen bada ingantaccen ilimi a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here