Gwamnatin Buhari ta Gaza Gurin Tsaro – Mohammed Umar Bago
Mohammed Umar Bago ya yarda gazawar Buhari a kan tsaro ta fito fili.
Bago ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi maganin miyagun ‘yan bindiga.
‘Dan Majalisar ya ce ba a fadawa Buhari gaskiya, ko ya yi kunnen-kashi.
Hon. Mohammed Umar Bago ya yi magana bayan ‘yan majalisar wakilai sun yi wani zama da sufetan ‘yan sandan Najeriya a kan sha’anin tsaro.
Mohammed Umar Bago mai wakiltar Chanchaga ya zanta da RfI Hausa inda ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza.
“Alal-hakika an yi daidai idan aka ce mun yi shiru, domin gwamnatinmu na APC ta kasa a kan maganar tsaro.” Inji ‘dan majalisar na jam’iyyar APC.
Umar Bago ya kara da cewa: “Abin da ya sa shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari bai samu masu fada masa gaskiya ba, ko kuma ya na ji, ya ki ya ji.”
Read Also:
‘Dan siyasar ya ce ganin yadda aka bar ‘yan bindiga suna cin karensu babu babbaka, amma aka shawo kan #EndSARS, ya nuna ba da gaske ake yi ba.
“Yau mako daya kenan kullum sai an tare mutane a hanyar Abuja. Yanzu ace ba za a fito da sojoji da ‘yan sanda a shiga dajin nan a kai sa kasa baki daya ba?”
A cewar Hon. Bago, tsefe dajin Kaduna zuwa Abuja bai fi karfin jami’an tsaron Najeriya ba, amma an gagara yi, ya bada shawarar a ba sha’anin tsaro karfi.
“Mu je wasu kasashe mu nemo wadanda za su taya mu (yaki), amma mu na kallo a zo har gidajenmu a yankamu, wannan abin fa ba abu mai kyau ba ne.”
“Siyasa ai riga ce, idan ka ga dam aka cire jam’iyya. Maganar ‘Dan Najeriya ake yi.”
Ya ce: “Mu na kallo, ba ka iya kwanciya a gidanka, ni daga Neja na ke.”
Ya ce ana kallon miyagu suna yawo kan babura da bindigogi amma babu abin da aka yi. Bago ya ce laifin ba na IGP ba ne, matsalar ta na kan shugaban kasa.