Gwamnatin Kaduna ta Rusa Otel Akan Saba Dokokin Jahar

A karshe, an yi lebur da gidan da aka shirya banbadewa a jihar Kaduna.

Hukumar KASUPDA ta ce an rusa gidan ne saboda sun saba dokokin da gwamnati ta shimfida.

Gwamnatin Kaduna ta bada umurnin rufe makarantu sakamakon waiwayen Korona ta biyu Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan otel ɗin da aka yi shirya gudanar da taron banbadewa zindir farkon makon nan a unguwar Barnawa dake jihar.

Hukumar cigabar cikin garin Kaduna KASUPDA ta bayyana cewa an rusa gidan badalar ne bayan gudanar da bincike kan wajen.

KASUPDA ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook inda ta daura hotunan yadda aka ruwa waje.

A cewar, mammalakan dakin Otal din mai suna Asher dake Unguwar Barnawa sun saba dokokin hana yaduwar cutar Korona da gwamnatin jihar ta gindaya duk da gargadi da barazanar da gwamnan jihar yayi.

Hakazalika otal din aka shirya wannan taron banbadewa tsirara da aka shirya a jihar.

Hukumar tace: “KASUPDA ta rusa Asher Hotel dake Barnawa, karamar hukumar Kaduna ta kudu.” “Asher Hotel ya kasance wurin da aka shirya taron holewa zindir.

Hakazalika an damke gidan da saba dokar hana yaduwar COVID-19 da hukumar ta shimfida.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here