Gwamnatin Jahar Kaduna ta Yantar da Bursunoni 12

A yayin bikin shiga sabuwar shekara, gwamnan jahar Kaduna ya yiwa Bursunoni 12 afuwa.

A cewar Muyiwa Adekeye, mai bashi shawara na musamman kan labarai da sadarwa, Gwamna El-Rufai ya bayar da umurnin sakinsu.

Adekeye ya bayyana cewa sakin Bursunonin na bisa shawarar wani kwamitin bayar da shawarwari.

Domin murnar shiga sabuwar shekara, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi umurnin sakin Bursunoni 12 daga cibiyoyin gyara hali a jahar, jaridar The Cable ta ruwaito.

A wata sanarwa daga Muyiwa Adekeye, mai ba E-Rufai shawara na musamman a kafofin watsa labarai da sadarwa, ya nuna cewa an yi wa wadanda suka ci moriyar shirin bisa ga shawarar kwamitin bayar da shawarwari kan afuwa.

Rabe-raben fursunonin da aka saki sun hada da fursunoni 10 wadanda ya rage watanni shida ko kasa da haka su kammala wa’adin shekaru uku da aka yanke masu, Yayinda aka yiwa mutum biyu afuwa saboda shekaru.

Adekeye ya yi bayanin cewa wannan hukunci ya kasance bisa karfin iko da kundin tsarin mulki ya baiwa gwamnan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here