Kano: Gwamnatin Jahar ta ƙwace Filaye 400 Daga Hannun Mutane
Gwamnatin jahar Kano ta bayyana cewa ta ƙwace filaye 400 daga hannun wasu mutane ta maida ma asalin waɗanda suka mallake su.
Shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci na jahar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado ne ya sanar da haka a hedkwatar hukumar.
Ya kuma ƙara da cewa sun ƙwato maƙudan kuɗaɗe da aka karkatar dasu ta hanyar da bata dace ba a cikin wannan shekarar.
Hukumar dake kula da ƙorafe-ƙorafen jama’a da yaƙi da cin hanci ta jahar Kano (PCACC) ta ƙwace filaye kimanin 400 daga hannun wasu mutane a faɗin jahar.
Ta kuma bayyana cewa yawan filayen ta ƙwace su ne ta maidama asalin waɗanda suka mallaki filayen, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana haka a wani taron haɗin guiwa da ya gudana a hedkwatar hukumar ranar Laraba.
Read Also:
Shugaban ya ƙara da cewa hukumarsa ta ƙwato maƙudan kuɗaɗe da suka wuce N521,964,122. Rimingado, ya bayyana cewar hukumar su ta samu korafe-korafe 2256 daga wajen jama’a cikin wannan shekarar da muke ciki.
Ya ce hukumar ta samu nasarar gano wuraren ajiya inda aka ajiye kayayyaki masu muhimmanci na biliyoyin nairori da aka kwace amma daga baya aka sake su bayan tattaunawa da yan kasuwar.
Rimingado yace:
“Mun kwato filaye 400 daga hannun wasu mutane kuma mun maida su ga asalin waɗanda suka mallaki filayen a sassa daban-daban na jahar nan.”
“Mun kuma shiga tsakani, mun sulhunta matsalolin tsaro 60 tsakanin makiyaya da manoma, wanda mafi yawancin su a kan kiyo ne.”
Rimingado yace dayawan mutane ana kaisu kotu kan rikicin da basu ji ba basu gani ba, musamman a ƙananan hukumomin Ɗanbatta, Ɓagwai da Kuma Tudun Wada.
Ya kuma ƙara jaddada cewa hukumar su zata cigaba da aiki yadda yakamata don ƙara tabbatar da Kano a cikin jihohin farko a fannin yaƙi da cin hanci da rashawa.