Gwamnatin Kano Tayi Sabon Naɗe a CARS da SRCOE
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi muhimman nade. nade a gwamnatin jihar Kano.
Daga cikin nade-naden da Ganduje ya yi akwai nadin shugaban makarantar CARS da SRCOE.
Ganduje ya bukaci mutanen da aka nada da su yi aiki tukuru wajen sauke nayin da aka dora a kansu.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Dr Yusuf Musa a matsayin Provost ɗin makarantar share fagen shiga jami’a(CARS).
Ganduje ya kuma naɗa Saminu Bello a matsayin Rejistara Kwalejin Ilmi ta Sa’adatu Rimi (SRCOE).
Read Also:
Acewar babban sakataren yaɗa labarai (CPS), Gwamna Ganduje ya naɗa Garba Baƙo Gezawa a matsayin magatakarda (Clerk) na majalisar jihar Kano.
“Dole ku yi aiki tukuru domin samun nasara da cigaban Jihar Kano. Amfani da fasahar zamani ya zama tilas a al’amurran da suka shafi hukuma a yau”, Ganduje ya gayawa sabbin waɗanda ya naɗa.
“Saboda haka, ku yi aiki tuƙuru da dabarun fasahar bayanai na zamani, kamar yadda ake yi a duniya” a cewarsa.
Ya kuma shawarcesu akan su haɗe kansu, su zama tsintsiya, inda ya tuna musu cewa; “haɗin kai da aiki da juna na kaiwa ga cimma babbar Nasara”.