Kasafin Kudin 2021: Abinda Gwamnatin Legas Zata Kashe a Wannan Shekarar
Gwamnatin Legas ta sa hannu a kan kasafin kudin shekara mai zuwa.
Jihar Legas za ta batar da Naira Tiriliyan 1.163 a shekarar nan ta 2021.
Wannan kudi ya zarce abin da rabin jihohin Arewa za su batar a bana.
A ranar Alhamis, 31 ga watan Disamba, 2020, mai girma gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sa hannu a kan kundin kasafin kudin shekarar 2021.
Jaridar Vanguard ta rahoto Babajide Sanwo-Olu ya rattaba hannu a kasafin kudin N1.163 da ake sa ran gwamnatin Legas za ta kashe a shekarar bana.
Read Also:
An ware 40% na wannan kasafin kudi ta yadda za a kashe biliyan N460 wajen biyan albashi da alawus da sauran abubuwan batarwan yau da gobe.
Gwamnatin Legas za ta kuma batar da Naira biliyan 702.9 wajen yin ayyukan more rayuwa a 2021.
A duk jihohi babu wani gwamna da ya yi kasafin kudin da ya kama kafar na Legas, abin da jihar za ta kashe ya nunka na jihohi da-dama a dunkule.
Kamar yadda mu ka fahimta, kasafin kudin jihar Legas ya fi karfin abin da rabin jihohin Arewa za su kashe a wannan shekara ta 2021 da aka shiga jiya.
Sai an hada kasafin jihohin Nasarawa, Benuwai, Kogi, Gombe, Yobe, Kebbi, Zamfara, Jigawa da Adamawa, sannan za a samu abin da Legas za ta kashe.
Abin da wadannan jihohi tara da aka ambata su ka yi kasafi a bana shi ne N115bn, N10bn, N134bn, N116bn, N140bn, N107bn, N141bn, N145bn, da N156bn.