Sheikh Gumi ya yi Kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Samar da Ma’aikatar da za ta Dinga Kula da Lamurran Makiyaya

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Dr Ahmad Gumi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ma’aikatar da za ta dinga kula da lamurran makiyaya don kawo karshen matsalolinsu.

Ya fadi hakan ne yayin jawabi ranar Laraba a taron makiyaya da bada tsaro ga Fulani wanda ya gabata na kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya da kungiyar sasanci ta arewa suka gabatar a Abuja.

Haka zalika, shugaban kungiyar MACBAN, Husseini Bosso ya koka a kan irin kalubale da suke fuskanta a harkar noma da kiwonsu amma duk da haka gani ake kamar su ne ke da alhaki a ta’addanci bayan su yafi shafa.

Abuja- Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musuluncin nan, ya yi kira ga gwamnatin tarayya samar da ma’aikatar da za ta dunga lura da lamurran makiyaya don kawo karshen matsalolinsu.

Gumi ya fadi hakan ne a ranar Laraba a ‘taron makiyaya da bada tsaro ga Fulani ‘, wanda ya gabata a Abuja mai taken, ‘Mafita ga kalubalen tsaro ga makiyaya da Fulani a Najeriya.’

Kungiyar Miyetti Allah ta makiyayan shanu da Kungiyar Sulhu ta arewa (NCM) ne suka shirya taron, The Cable ta rawaito.

“Ya kamata gwamnati ta maida hankalinta a kan wadannan mutanen saboda yadda suke yawan bayyana damuwarsu,” NAN ta yanko maganarsa inda yake cewa.

“Abun da na tsammata daga gwamnati bai gaza da abun da tayi ba, a lokacin da matasan Neja Delta na barnatar da tattalin arzirki.

“Wadannan mutanen suma suna addabar arzikin noman Najeriya wanda shi ne tushen tattalin arzirkin kasar.

“A ganina akwai bukatar gwamnati ta kara kulawa. Suna bukatar a mai da hankali a kansu. Mafi karancin abun da suke bukata shine ma’akatar da zata lura da lamarinsu.”

Husseini Bosso, shugaban MACBAN na kasa, yayin jawabinsa, ya ce ya wuce a ce labari ne garkuwa da mutane da fashi da makami wanda ya zama ruwan dare a yankuna da dama a kasar nan.

Sai dai, Bosso ya ce ba gaskiya bane jita-jitar da ake yadawa na cewa makiyaya ne ke da alhakin wadannan ta’addancin, suma makiyayan na fuskantar kalubalen.

“Abun takaici shi ne yadda ba a yada duk wani farmaki da ya ritsa da makiyaya a yanar gizo. Mutanenmu sun fi kowa fuskantar matsalar tsaro,” a cewarsa.

“Cikin kwanakin nan aka yi garkuwa gami da halaka shugabannin MACBAN na Kogi, Neja, Nasarawa da shugabannin kananan hukumomi biyar, wadanda suka hada da gundumar Gwagwalada.

“Hakan na nuna cewa ba mu tsira daga matsalolin garkuwa da mutane da fashi da makami a yankunanmu ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here