Gwamnatin Tarayya: Dalilin Tashin Farashin Man Fetur

Karamin ministan fetur, Timipre Sylva, ya fadi dalilin tashin farashin mai.

A cewarsa, tun bayan da Pfizer suka bayyana riga-kafin cutar COVID- 19 komai ya tashi.

Ya kara da cewa, matsawar farashin mai ya tashi, farashin komai yana tashi.

Karamin ministan fetur, Timipre Sylva, ya ce tashin farashin man fetur ya auku ne saboda wani kamfanin hada magunguna na Amurika, Pfizer ya bayyana riga-kafin cutar COVID-19.

Sylva ya fadi hakan ne a wata ganawar sirri da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ranar Lahadi, inda ya sanar da manema labarai cewa samun riga kafin cutar COVID-19 shine sanadiyyar tashin kudin man fetur a kasuwannin duniya.

“Tashin farashin man fetur ya auku ne sakamakon sanar da riga-kafin cutar COVID-19 da Pfizer sukayi. Idan an lura, farashin ya karu ne bayan sanar da samuwar riga-kafin.

“Matsawar kudin mai ya tashi, yana nufin farshin sauran kayan masarufi ya karu, haka kuma duk wani abu da aka tace, kudinsa zai karu,” a cewarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here