Gwamnatin Tarayya ta Fayyace Batun Shekarun Zana WAEC/NECO

 

Abuja – Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagoranci Bola Ahmed Tinubu ta yi ƙarin haske kan batun mafi ƙarancin shekarun zana jarabawar gama sakandire a Najeriya.

Rahotannin da ke yawo sun yi iƙirarin cewa gwamnatin ta yanke cewa dole sai ɗalibi ya kai shekaru 18 gabanin a ba shi damar zana jarabawar WAEC da NECO.

Gwamnatin tarayya ta fayyace batun WAEC/NECO

Sai dai gwamnatin Tinubu ta musanta raɗe-raɗin inda ta ce jarabawar JAMB ta share fagen shiga jami’o’i ce ta sanyawa mafi ƙarancin shekaru 18, rahoton Punch.

Leadership ta ce ƙaramin ministan ilimi, Dr. Tanko Sununu ne ya bayyana hakan yayin zantawa da ƴan jarida ranar Jumu’a a Abuja.

Ya ce gwamnati dai ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi karancin shekarun zana jarabawar UTME wacce hukumar JAMB ke shiryawa.

UTME: Matakin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka

“Game da wannan batun, mun riga mun yi bayani ba sau ɗaya ba, babu wurin da ministan ilimi, Tahir Mamman ko ƙaramin minista suka yi maganar ƙarancin shekarun zama WAEC, NECO ko NABTEB.”

Jama’a sun tsinci wasu kalamai daga jawabin minista, suka masa gurguwar fassara cewa an ƙayyade shekarun WAEC da NECO.

“Abin da muka faɗa a baya shi ne shekarun shiga jami’a da jarabawar UTME, mun yi bayani mai gamsarwa kuma matakin ya yi daidai da tsarin ilimin ƙasar nan.”

– Tanko Sanunu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here