Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya ta Sanya Ranar Sake Ganawa da ASUU
FCT, Abuja – Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta tabbatar da cewa gwamnati da kusoshin ASUU za su sake ganawa a ranar Laraba, 11 Satumba, 2024.
Wannan na zuwa bayan kungiyar ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki matukar gwamnatin Tinubu ta ci gaba da watsi da yarjejeniyar da aka cimma a baya.
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa a zaman da aka yi tsakanin ASUU da kwamitin gwamnati karkashin jagorancin Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, an samu nasara
ASUU da gwamnati: An kafa kwamiti
Read Also:
Mataimakin shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Chris Piwuna ya bayyana cewa an kafa kwamitin da zai yi duba kan batun IPPIS da sauran matsalolin albashin da ake bin gwamnati.
Ya ce an cimma matsayar ne bayan taron baya-bayan nan da ya gudana, karkashin jagorancin Ministan Ilimi, Tahir Mamman.
“Batun ASUU dadadde ne,” Gwamnati
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa wasu daga cikin bukatun da ASUU ke neman gwamnati ta biya mata sun dade, wasu tun daga shekarar 1981 ake neman a samar da su.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya kara da cewa amma da yawa daga cikin bukatun da ASUU ke bukata, tuni shugaban kasa ya fara kokarin magance su.